Zikirin safe

Aika ta WhatsApp
Danna blue button don rage counter
Mun shiga wata sabuwa kuma da ita dukkan mulki na Allah ne. Godiya ta tabbata ga Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, wanda ba ya da abokin tarayya. Mulki na Allah ne, kuma gõdiya ta tabbata a gare Shi, kuma Shi, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne. Ya Ubangiji ina rokonka alherin wannan rana da na ranakun da ke bayanta, kuma ina neman tsarinka daga sharrin wannan rana da na ranakun da ke bayanta. Ya Ubangijina, ina neman tsarinka daga kasala da tsufa mara ƙarfi. Ya Ubangijina, ina neman tsarinka daga azabar wuta, da azabar kabari.
أصبحنا وأصبح الملك لله، والحمد لله، لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير، ربّ أسألك خير ما في هذا اليوم وخير ما بعده وأعوذ بك من شر ما في هذه الليلة وشر ما بعدها ربّ أعوذ بك من الكسل وسوء الكبر، ربّ أعوذ بك من عذاب في النار وعذاب في القبر.
'Asbahnaa wa 'asbahal-mulku lillaahi walhamdu lillaahi, laa 'ilaaha 'illallaahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu wa Huwa 'alaa kulli shay'in Qadeer. Rabbi 'as'aluka khayra maa fee haathal-yawmi wa khayra maa ba'dahu wa 'a'oothu bika min sharri maa fee haathal-yawmi wa sharri maa ba'dahu, Rabbi 'a'oothu bika minal-kasali, wa soo'il-kibari, Rabbi 'a'oothu bika min 'athaabin fin-naari wa 'athaabin fil-qabri.
Ya Allah kai ne Ubangijina, babu abin bautawa da gaskiya sai kai. Ka halicce ni kuma ni bawanka ne. Ina kiyaye alkawarinka, da alkawarina gare ka gwargwadon iko. Ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata. Ina shigar da ni'imarKa gare ni, kuma ina shigar da laifuffukana. Ka gafarta mini, domin babu mai gafarta zunubai face Kai.
اللهـم أنت ربـي لا إله إلا أنت ، خلقتنـي وأنا عبـدك ، وأنا علـى عهـدك ووعـدك ما استـطعـت ، أعـوذبك من شـر ما صنـعت ، أبـوء لـك بنعـمتـك علـي وأبـوء بذنـبي فاغفـر لي فإنـه لا يغـفر الذنـوب إلا أنت .
Allaahumma 'Anta Rabbee laa 'ilaaha 'illaa 'Anta, khalaqtanee wa 'anaa 'abduka, wa 'anaa 'alaa 'ahdika wa wa'dika mas-tata'tu, 'a'oothu bika min sharri maa sana'tu, 'aboo'u laka bini'matika 'alayya, wa 'aboo'u bithanbee faghfir lee fa'innahu laa yaghfiruth-thunooba 'illaa 'Anta.
Ya Allah na shiga wata sabuwar safiya ina kira gareka da ma'abuta Al'arshinka da mala'ikunka da dukkan halittu domin su shaida lallai kai ne Allah , babu abin bautawa da gaskiya sai kai kadai , ba ka da abokin tarayya . , kuma lalle Muhammadu bawanka ne kuma manzonka . (Karanta sau hudu cikin Larabci).
اللهـم إنـي أصبـحت أشـهدك ، وأشـهد حملـة عـرشـك ، وملائكتك ، وجمـيع خلـقك ، أنـك أنـت الله لا إله إلا أنـت وحـدك لا شريك لـك ، وأن محمـدا عبـدك ورسـولـك.
Allaahumma 'innee 'asbahtu 'ush-hiduka wa 'ush-hidu hamalata 'arshika, wa malaa'ikataka wajamee'a khalqika, 'annaka 'Antallaahu laa 'ilaaha 'illaa 'Anta wahdaka laa shareeka laka, wa 'anna Muhammadan 'abduka wa Rasooluka.
Ya Allah duk wata ni'ima da aka samu a wurina ko wani daga cikin halittunka to daga gare ka ne kadai ba ka da abokin tarayya . Dukkan yabo ya tabbata a gareka kuma godiya ta tabbata a gareka.
اللهـم ما أصبـح بي مـن نعـمة أو بأحـد مـن خلـقك ، فمـنك وحـدك لا شريك لـك ، فلـك الحمـد ولـك الشكـر.
Allaahumma maa 'asbaha bee min ni'matin 'aw bi'ahadin min khalqika faminka wahdaka laa shareeka laka, falakal-hamdu wa lakash-shukru.
Allah ma'ishina ne . Bãbu wani abin bautãwa fãce Shi. Na dogara gare Shi, Shi ne Ubangijin Al'arshi maɗaukaki.
حسبـي الله لا إله إلا هو علـيه توكـلت وهو رب العرش العظـيم.
Hasbiyallaahu laa 'ilaaha 'illaa Huwa 'alayhi tawakkaltu wa Huwa Rabbul-'Arshil-'Adheem
Da sũnan Allah, Wanda bãbu abin da yake cũtar a cikin ƙasa, kuma a cikin sammai da sũnanSa, kuma Shĩ ne Mai ji, Masani.
بسـم الله الذي لا يضـر مع اسمـه شيء في الأرض ولا في السمـاء وهـو السمـيع العلـيم.
Bismillaahil-lathee laa yadhurru ma'as-mihi shay'un fil-'ardhi wa laa fis-samaa'i wa Huwas-Samee 'ul- 'Aleem .
Ya Allah da kai muke shiga safiya kuma da kai muke shiga marece, da kai muke rayuwa kuma da kai muke mutuwa, kuma zuwa gareka makmama take.
اللهـم بك أصـبحنا وبك أمسـينا ، وبك نحـيا وبك نمـوت وإلـيك النـشور.
Allaahumma bika 'asbahnaa, wa bika 'amsaynaa, wa bika nahyaa, wa bika namootu wa 'ilaykan-nushoor.
Mun shiga wata sabuwar rana akan addinin musulunci na dabi'a, kalmar Ikhlasi, addinin Annabinmu Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam), da imanin Babanmu Ibrahim. Ya kasance mai karkata zuwa ga Allah, kuma musulmi. Kuma bai kasance daga waɗanda suke bauta wa wanin Allah ba.
أصبـحـنا على فطرة الإسلام، وعلى كلمة الإخلاص، وعلى دين نبينا محمد صلى الله عليه وسلم، وعلى ملة أبينا إبراهيم حنيفا مسلما وما كان من المشركين.
Asbahnaa 'alaa fitratil-'Islaami wa 'alaa kalimatil-'ikhlaasi, wa 'alaa deeni Nabiyyinaa Muhammadin (sallallaahu 'alayhi wa sallama), wa 'alaa millati 'abeenaa 'Ibraaheema, haneefan Musliman wa maa kaana minal-mushrikeen.
Ya Allah ka karamana lafiya a jikina. Ya Allah ka kiyaye min ji na. Ya Allah ka kiyaye min ganina. Babu abin bautawa face Kai.
اللهـم عافـني في بدنـي ، اللهـم عافـني في سمـعي ، اللهـم عافـني في بصـري ، لا إله إلا أنـت.
Allaahumma 'aafinee fee badanee, Allaahumma 'aafinee fee sam'ee, Allaahumma 'aafinee fee basaree, laa 'ilaaha 'illaa 'Anta .
Ya Allah ina neman tsarinka daga kafirci da talauci kuma ina neman tsarinka daga azabar kabari . Babu abin bautawa face Kai.
اللهـم إنـي أعـوذ بك من الكـفر ، والفـقر ، وأعـوذ بك من عذاب القـبر ، لا إله إلا أنـت.
Allaahumma 'innee 'a'oothu bika minal-kufri, walfaqri, wa 'a'oothu bika min 'athaabil-qabri, laa 'ilaaha 'illaa 'Anta.
Ya Allah ina neman gafararka da tsarinka duniya da lahira. Ya Allah ina neman gafararKa da tsarinka a cikin addinina da al'amurana na duniya da iyalana da dukiyoyi na. Ya Allah ka rufa min asiri, ka kiyaye ni daga bacin rai. Ya Allah ka kiyayeni daga abinda ke gabana da bayana, da damana, da haguna, da samana. Ina neman tsarinka da girmanka da kada a kashe ni daga karkashina.
اللهـم إنـي أسـألـك العـفو والعـافـية في الدنـيا والآخـرة ، اللهـم إنـي أسـألـك العـفو والعـافـية في ديني ودنـياي وأهـلي ومالـي ، اللهـم استـر عـوراتي وآمـن روعاتـي ، اللهـم احفظـني من بـين يدي ومن خلفـي وعن يمـيني وعن شمـالي ، ومن فوقـي ، وأعـوذ بعظمـتك أن أغـتال من تحتـي.
Allaahumma 'innee 'as'alukal-'afwa wal'aafiyata fid-dunyaa wal'aakhirati, Allaahumma 'innee 'as'alukal-'afwa wal'aafiyata fee deenee wa dunyaaya wa 'ahlee, wa maalee , Allaahum-mastur 'awraatee, wa 'aamin raw'aatee, Allaahum-mahfadhnee min bayni yadayya, wa min khalfee, wa 'an yameenee, wa 'an shimaalee, wa min fawqee, wa 'a'oothu bi'adhamatika 'an 'ughtaala min tahtee.
Ya Rayayye, Ya Madawwamiyar, da rahamarKa nake kira gare Ka da Ka daidaita dukkan al'amura na. Kada ka sanya ni a kan raina ko da kiftawar ido (wato dan lokaci kadan).
يا حيّ يا قيّوم برحمتك أستغيث، أصلح لي شأني كلّه ولا تكلني إلى نفسي طرفة عين.
Yaa Hayyu yaa Qayyoomu birahmatika 'astagheethu 'aslih lee sha'nee kullahu wa laa takilnee 'ilaa nafsee tarfata 'aynin.
Ya Allah Masanin fake da bayyane, Mahaliccin sammai da kassai Ubangijin komai da ma'abucinsa , ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai kai . Ina neman tsarinka daga sharrin raina da sharrin Shaidan da mataimakansa . (Ina neman tsarinka) da ka jawo wa raina sharri da cutar da kowane musulmi.
اللهـم عالـم الغـيب والشـهادة فاطـر السماوات والأرض رب كـل شـيء ومليـكه ، أشهـد أن لا إلـه إلا أنت ، أعـوذ بك من شـر نفسـي ومن شـر الشيـطان وشركه ، وأن أقتـرف علـى نفسـي سوءا أو أجـره إلـى مسـلم.
Allaahumma 'Aalimal-ghaybi wash-shahaadati faatiras-samaawaati wal'ardhi, Rabba kulli shay'in wa maleekahu, 'ash-hadu 'an laa 'ilaaha 'illaa 'Anta, 'a'oothu bika min sharri nafsee, wa min sharrish-shaytaani wa shirkihi, wa 'an 'aqtarifa 'alaa nafsee soo'an, 'aw 'ajurrahu 'ilaa Muslimin.
Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da Ya halitta.
أَعـوذُ بِكَلِمـاتِ اللّهِ التّـامّـاتِ مِنْ شَـرِّ ما خَلَـق.
'A'oothu bikalimaatil-laahit-taammaati min sharri maa khalaqa.
Ya Allah muna rokonka tsira da aminci ga annabinmu Muhammadu
اللهم صل وسلم وبارك على نبينا محمد.
Allahumma salli wa sallim 'alaa nabiyyinaa Muhammadin
Ya Allah ina rokonka ilimi mai amfani da guzuri mai kyau da ayyukan karbabbe.
اللهم إني أسألك علما نافعا، ورزقا طيبا، وعملا متقبلا.
Allaahumma 'innee 'as'aluka 'ilman naafi'an, wa rizqan tayyiban, wa 'amalan mutaqabbalan.
Na yarda da Allah a matsayin Ubangijina, da Musulunci a matsayin addinina, kuma Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya zama Annabina.
رضيت بالله ربّاً، وبالإسلام ديناً، وبمحمّد صلى الله عليه وسلم نبيّاً.
Radheetu billaahi Rabban, wa bil-'Islaami deenan, wa bi-Muhammadin (sallallaahu 'alayhi wa sallama) Nabiyyan.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, wanda ba ya da abokin tarayya. Nasa ne mulki kuma gõdiya ta tabbata a gare shi, kuma Shĩ, a kan dukkan kõme, Mai ĩkon yi ne.
لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير.
Laa 'ilaaha 'illallaahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul-mulku wa lahul-hamdu, wa Huwa 'alaa kulli shay'in Qadeer.
Glory is to Allah and praise is to Him.
سُبْحـانَ اللهِ وَبِحَمْـدِهِ.
Subhaanallaahi wa bihamdihi.
Ina neman gafarar Allah da tuba zuwa gare shi.
أسْتَغْفِرُ اللهَ وَأتُوبُ إلَيْهِ
'Astaghfirullaaha wa 'atoobu 'ilayhi.
Number of Visitors:
Ana lodawa...
Messenger My Islamic library
Masba7a أضف إلى الشاشة الرئيسية